15 Satumba 2020 - 12:13
​Iran : Ma'aikatar Harkokin Waje Ta Gayyaci Jakadan Jamus A Tehran

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci Jakadan kasar Jamus a Tehran Mr Hansa-Udo Muzel zawa ma’aikatar don gargadi da kuma jan kunnensa kan irin sakonnin twitter da yake ta watsawa a kafafen sadawar ta internet dangane da ayyukan ma’aikatar shari’ar kasar.

ABNA24 : Darakta mai kula da al-amuran kasashen turai a ma’aikatar ya sadu da Jakadan kasar ta Jamus a safiyar yau Litinin ya bayyana bayyana masau sakonnin twitter da yay i ta yadawa a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata sun sabawa ayyukan diblomasiyya kuma shihsigi ne a cikin harkokin cikin gida na kasar Iran.

A jiya Lahadi ne jakadan kasar ta Jamus ya yi watsa sakonnin twitter inda yake allawadai da zartar da hukuncin kisa wanda ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta yi a kan wani dan kasar mai suna Navid Afkari bayan da kotu ta sami shi da laifin dabawa wani jami’in gwamnati wuka har ya kasheshi a shekara ta 2018.

A safiyau yau likitinin ce aka kashe mai laifin NAvid Afkari. Sanadiyyar wannan laifin. Afkari dan shekara 27 a duniya ya kasha Hassan Turkman ma’aikacin wani kamfanin samar da ruwa a kudancin birnin Shiraz a lokacin zanga-zangar Karin farshin man fetura a kasar a shekara ta 2018.

342/